
Al'adun Gargajiya
Halin da ake ciki game da al'adar 'Yan Kama da ke neman ɓacewa a ƙasar Hausa
Shirin "Al’adunmu na gado, ya mayar da hankali kan fadi-tashin da ake yi don adana tsohuwar al'adar mawaƙan 'Yan Kama a ƙasar Hausa. Waƙoƙin 'Yan Kama salon fasaha ne na musamman da mawaƙan ke amfani da shi domin nishaɗantarwa, inda suke sauya shahararrun waƙoƙi su koma na maganar abinci ko cika tumbi. A cikin shirin, masana sun bayyana yadda waɗannan mawaƙa ke da ƙwarewa wajen sarrafa harshen Hausa da sauya salon magana don juyata zuwa nishaɗi. Sai dai bincike ya nuna cewa wannan daɗaɗɗiyar al'ada tana dab da ɓacewa gaba ɗaya a wannan zamanin na yanzu. Babban dalilin da ya sa sana'ar ke mutuwa shi ne rashin gado, domin kuwa ko da su kansu 'ya'yan mawaƙan na 'Yan Kama ba sa sha'awar ɗaukar wannan sana'a don gadon iyayensu kamar yadda aka saba a baya.

