
Ilimi Hasken Rayuwa
Yadda matasa suka ƙera jirgi maras matuƙi mai cin Kilomita 30 a Kano
Shirin a wannan makon ya leka Kanon Najeriya, inda aka gano wani sabon tarihin bunkasar kimiyya da fasaha da matasan yankin ke jagoranta. Wannan gagarumar bajinta dai wani matashi Abubakar Waiya, wanda ya daɗe yana fafutukar kera na'urorin shawagi ne ya ƙera jirgi maras matuƙi domin taimakawa ɓangaren tsaro da kuma boma. Jirgin da ya kera a yanzu yana da ikon tashi da kansa har na tsawon kilomita 30 ba tare da ya ɓace ba. Wannan na'ura tana da aiyuka na musamman da aka tsara ta don yi, kamar feshin maganin ƙwari a gonaki na zamani da kuma kai magungunan gaggawa zuwa yankunan karkara da motoci ba su iya zuwa saboda rashin hanya. Duk da wannan gagarumar nasara, babban ƙalubalen da ke gaban matasan shi ne tsarin dokoki na ƙasa. Masu fafutuka na ganin cewa, idan har gwamnati da masu ruwa da tsaki suka ba wa waɗannan matasa dama da goyon baya, wannan ƙoƙari daga birnin Kano zai zama tushen samar da dabarun tsaro da aikin gona na zamani ga ɗaukacin yammacin Afirka. Tambayar da ta rage anan ita ce: Shin gwamnati za ta tallafa wa wannan fasaha ta gida don ta bunkasa, ko kuwa za a zura ido ta ɓace ne?

