
Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
Ra'ayoyi kan yadda rashin bin ƙa'idojin gini ya haifar da ambaliya a Abuja da Kano
A Najeriya duk da gargaɗin da hukumar yanayi ta NIMET ta riƙa yi a lokuta da dama game da ambaliyar da wasu sassan ƙasar zasu fuskanta a damunar bana, wajen ganin an ɗauki matakan daƙile illar da hakan zai haifar. Tuni aka ga wannan ambaliya a birane da dama ciki har da Abuja fadar gwamnatin ƙasar, birnin da ruwa ya shanye sassa da dama da ke matsayin ambaliya mafi muni da aka gani, wanda ake alaƙantawa da dalilai da dama ciki har da gine-gine kan magudanan ruwa, wannan na zuwa a dai dai lokacin da can a jihar Kano ma ake cike da fargabar makamanciyar ambaliyar.... Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

